Kenya

An samu wasu kaburbura a kasar Kenya

Yankin Tana da ake yawan rikici tsakanin 'Yan kabilar Pokomo da Orma
Yankin Tana da ake yawan rikici tsakanin 'Yan kabilar Pokomo da Orma Photo AFP/Simon Maina

‘Yan Sanda a kasar Kenya, sun ce sun gano wasu kaburbura guda biyu, da aka birne mutane da dama, wadanda aka kashe a rikicin kabilancin Yankin Tana Delta. A cewar ‘Yan Sandan, suna bukatar kotu ta bada umurnin damar hako gawawakin domin gudanar da bincike akai.  

Talla

Akalla mutane 100 aka kashe a rikicin kabilancin da aka kwashe wata guda ana yi a yankin, wanda ya lakume kujerar Ministan kasar.

“Mun gano kaburburan, kuma muna kyautata zaton za a samu wasu da dama, amma bam u san ko su wanene aka binne ba, amma ga dukkan alamu, za a samu karuwan yawan mutanen da su ka mutu a fadan fiye da yadda mu ke tsammani”, inji wani Dan sanda.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.