Afrika

Sharhin Jaridun Afrika

A cikin sharhin jaridun nahiyar Afrika, Jaridar, BusinessDay, ta rawaito cewa ma’aikata masu hako ma’adinai a mahakar Platinum da ke Marikana sun yadda da karin kashi 22 a matsayin karin da za a musu akan albashinsu, inda su ka yi alkawarin dawowa kan ayyukansu.

Taswirar nahiyar Afrika
Taswirar nahiyar Afrika www.vbmap.org
Talla

Sai dai Jaridar ta rawaito cewa, masana sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar sauran mahaka ma’adinan a kasar, suma su nemi karin albashi, wanda yarjejeniyar da aka yi da kungiyar kwadago a kasar ba ta ba da hurumin yin hakan ba.

Masana a cewar jaridar sun yi hasashen cewa hakan zai iya jawo hatsaniya a bangaren na hakar ma’adinai, kuma zai iya jawo rashin aikin yi a kasar.

Ita kuwa Jaridar The Star a kasar ta Afrika ta Kudu ta dauko labarinta ne daga kasar Afghanistan, inda, ‘Yan kasar su takwasa su ka rasa rayukansu a wani harin kunar Bakin - Wake da ya rutsa da su.

A cewar jaridar ta The Star, mamatan sun samu ajalinsu ne ta dalilin bore da ake yi bayan fitar da bayanan muzantawa addinin musulunci da wani fim dan kasar amuraka ya yi.

Ita kuwa Jaridar The Standard ta kasar Kenya, ta mai da hankali ne akan labarin hana ‘Yan jarida da aka yi zuwa bakin kaburburan da aka gano a yankin Tana River da ke fama da rikici tsakanin makiyaya da manoma.

Jami’an tsaro dai sun gano wasu kaburbura guda biyu, sai dai an hana ‘Yan jarida halartar wurin, a cewar jaridar.

Kungiyar ba da agaji ta Red Cross, ta tabbatar da aukuwan hakan, sai dai bata sami isa bakin kaburburan ba saboda jamai’an tsaro da ke gadin yankin.

Haka kuma jaridar ta The Standard ta rawaito cewa an kwace wayar salula guda goma daga wasu da ake zargin na da hanu a cikin lamarin.

Ita kuwa jaridar The Daily Nation da ke kasar ta Kenya,ta mai da hankalinta ne kan batun yiwuwar samun matsalar fitar da sakamakon jarabawa da za a rubuta, domin yajin aikin da malaman kasar ke yi.

Hukumar kula da jarabawa a kasar ta Kenya ta yi kashedin cewa ba za a iya kai shekarar karatu zuwa shekara mai zuwa ba.

Malaman makarantun Sakandare har da ma na Jami’oi a kasar sun shiga yajin aiki tun makwanni uku da su ka gabata, domin neman a masu karin albashi da kuma kyautata wuraren ayyukansu.

Babban labarin da jaridar The East African a yankin shi ne ta dauka shi nakan batun yiwuwar shiga kasar cikin hada hadar kasuwanci a kasashen Gabashin Afrika.

A cewar jaridar ta The East African, matsalolin kudi da rashin tsaro kan iya zama cikas ga kasar ta Sudan ta Kudu shiga tarayyar.

Kasar ta Sudan ta Kudu dai na da burin ta shiga kasuwannin gabashin Afrika, wacce ke da mutane akalla miliyan 133, sai dai matsalolin kudade da kuma matsalolin tsaro tsakanin Juba da Khartoum na barazana ga wannan buri na kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI