Najeriya

‘Yan bindiga sun harbe kwamishinan Shari’a a Najeriya

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

‘Yan bindiga a Maiduguri, sun hallaka kwamishinan shari’ar Jihar Barno, Zanna Malam Gana, a kauyan sa dake Bama. Wannan na zuwa ne kwana guda bayan harin da aka kaiwa Tsohon shugaban gandirebobin Nigeria, Ibrahim Jarma a Azare, inda aka raunana shi, kana kuma aka hallaka dogarin sa. 

Talla

“Mun samu bayanan rasuwar kwamishinan shari’a Zannah Malam Gana, wasu mutane dauke da bindiga ne su ka harbe shi a gidansa da misalin 8:45 na yamma a daren jiya” inji wani Jami’in gwamnati.

Shi kuwa Shugaban gandirobobin, an kashe ne a Jihar Bauchi a yayin da ya ke barin masallaci zuwa gidansa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.