Saliyo

Cutar Amai da gudawa ta kashe mutane sama da 200 a Saliyo

masu fama da cutar amai dagudawa a  Congo
masu fama da cutar amai dagudawa a Congo AFP/ WALTER ASTRADA

Kungiyar Red Cross a kasar Saliyo tace akwai bukatar taimakon kudade domin a kawar da cutar amai da gudawa dake ta bazuwa a sassan kasar, wadda ya zuwa yanzu tasa aka yi hasarar rayukan mutane akalla 271.Uwar kungiyar agajin ta Red Cross ta fadawa manema labarai a Geneva cewa, cutar nata kara bazuwa yanzu haka a kasar.Kungiyar tace kakaf a nahiyar Africa cutar cholera ta kasar Saliyo tafi tsanani yanzu haka.