Afrika ta Kudu

Zuma ya musanta zargin cewa baya tare da mutanensa

Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Jacob Zuma a taron tarayyar kasashen Afrika
Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Jacob Zuma a taron tarayyar kasashen Afrika Reuters/Tiksa Negeri

Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Jacob Zuma, ya yi watsi da sukar da ‘Yan adawa ke yi na cewa ya yi watsi da mutane, inda ya yi ikrarin cewa, abokin hamayyarsa, Julius Malema, bashi da tasari a siyasar kasar sai dai cacar baki kawai da ya iya.

Talla

Shugaban kasar ta Afrika ta Kudu, Jacob Zuma, a yayin da ya ke ganawa da shugabannin kungiyar nahiyar turai, jim kadan bayan an kawo karshen yajin aikin da mahaka ma’adinan Kamfanin Lonmin ke yi a kasar, ya yi dariya ne a lokacin da aka nemi ya yi tsokaci ce game da zargin da ake yi na cewa ya yi watsi da ‘Yan jamiyarsa ta ANC da kuma mutanen da su ka zabeshi.

A cewar Zuma, wannan magana da ake yi ba gaskiya ba ce domin a koda yaushe ya na tare da mutanensa, inda ya kara da cewa masu wannan magana basu da hujja kwakwara.

An dai dade ana zargin shugaba Zuma da rashin daukan matakin gaggawa a lokacin da mahaka ma’adinai na Marikana su ka yi yi yajin aiki duk da cewa an kashe mutane 35.

Hakan ya sa aka tambayi shi dangantarkarsa da daya daga cikin manyan shugabannin kamfanin Lonmin da ake kira Cyril Ramphosa, inda Zuma ya ka da baki ya ce, Cyril Ramphosa, mamba ne na kwamitin zartasawa a jam’iyar ANC.

A lokacin da aka tambayi Zuma ko yaya ya ke ji game da sukar da abokin hamayyarsa Julius Malema ya ke mai, musamman irin goyon baya daya kan nunawa, mataimakin shugaban kasa Kgalema Motlanthe

Sai shugaban kasar ta Afrika ta Kudu ya ce ai Malema ba dan jam’iyar ANC bane, inda ya kara da cewa tuni an koreshi daga jam’iyar, kuma yanzu haka bashi da tasari, sai cacar bai kawai da ya iya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI