Cote d'Ivoire

Cote d’Ivoire za ta bude sararin samaniyarta da Ghana

Kasar Cote d’Ivoire ta ce zata bude sararin samaniyar ta da Ghana, bayan harin da aka kaiwa dakarun dake aiki kan iyaka, sai dai tace za’a cigaba da rufe hanyoyin shiga kasashen biyu ta ruwa da kasa, na zuwa wani lokaci. Wani hari da ‘Yan bindiga suka kai wajen binciken ababan hawa yayi sanadiyar hallaka mutane da dama, abinda ya sa aka rufe iyakokin.  

Shugaban kasar Cote d'Ivoire  Alassane Ouattara
Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara REUTERS/Charles Platiau
Talla

Fadar shugaba, Alassane Ouattara, tace za’a bude sararin samaniyar daga yau litinin.

Shugaba Ouattar dai na zargin magoya bayan tsohon shugaba kasar, Laurent Gbagbo, da kawo hare-hare wanda masu kaisu ke samu taimako daga 'Yan kasar Cote d'Ivoire da suka samu mafaka a kasar Ghana.

Dubban magoya bayan Gbagbo ne dai su ka tsere zuwa kasar Ghana bayan faduwar gwamnatinsa a rikicin day a lakume rayukan mutane sam da 3,000.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI