Mali

ECOWAS da Mali sun amince da aikawa da dakaru 3,300 cikin kasar

Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma tare da kasar Mali, sun amince akai dakarun samar da zaman lafiya 3,300 cikin kasar, dan taimaka mata kwato Yankin arewacin kasar.

Daga Hagu Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou, Shugaban kasar Burkina Faso  Blaise Compaore, Shugaban kasar Ivory Coast  Alassane Ouattara da shugaban kasar Benin Thomas Boni Yayi a wani Taron kasashen kungiyar ECOWAS
Daga Hagu Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou, Shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore, Shugaban kasar Ivory Coast Alassane Ouattara da shugaban kasar Benin Thomas Boni Yayi a wani Taron kasashen kungiyar ECOWAS REUTERS/Thierry Gouegnon
Talla

Ministan tsaron Mali, Yamoussa Camara ya sanar da haka, bayan ganawara da sukayi da takwaransa na Cote d’Ivoire, Paul Kofi Kofi, inda suke cewa, sun amince a girke dakarun a birnin Bamako.

Har yanzu dai ECOWAS na jiran umurni daga Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, dan samun goyan baya.

“Yanzu haka mali na tare da ECOWAS bayan an tattauna akan batutuwa da yawa” inji Camara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI