Egypt

Obama ya yabawa Morsi, saboda kare ofishin jakadancin Amurka

Shugaban Kasar Amurka, Barack Obama, ya aike da sakon godiya ga takwaransa na Masar, Mohammed Morsi, saboda kariyar da ya baiwa ofishin Jakadancin kasar, yayin zanga zangar adawa da kasar ta Amurka. 

Shugaban kasar Egypt, Mohammed Morsi
Shugaban kasar Egypt, Mohammed Morsi REUTERS/Suhaib Salem/Files
Talla

Wata wasika da Obama ya aikewa shugaba Morsi, shugaban ya dada yin suka da fim din da ya tinzira al’ummar Musulmin duniya, inda ya bayyana fatar sa na aiki tare da shugaba na Masar.

Idan dai ba’amanta ba, masu zanga zangar sun tsalaka katangar ofishin inda suka kona tutar Amurka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI