Kamaru

An kama mutane biyar da sassan jikin Dan Adam a Kamaru

Tutar kasar Kamaru
Tutar kasar Kamaru unimaps.com

‘Yan Sanda a kasar Kamaru, sun yi nasarar kama wasu mutane biyar da ake zargi da fataucin sassan jikin Bil Adama da na dabbobi. Kakakin wata kungiyar fararen hula, Eric Kabah Tah, yace an kama wasu matasa uku a garin Djoum, dauke sassan jikin Dan Adam da kuma na giwa a cikin jaka, cikin su harda kan mutum.  

Talla

Daga bisani matasan sun bada sunayen abokan huldar su biyu, kuma suma an danke su.

Bincike farko da aka gudanar ya nuna cewa, sassa jikin na mutum da kuma giwar za a kais u ga wani mutum ne muhimmi a garin Yaounde ne.

A Afrika ta Tsakiya, akan yi amfani da sassa jiki wajen tsafe-tsafe inda mutanen da ke yin hakan na tunanin mutum zai iya samun daukaka.

Yawanci akan tono su ne daga kabarurruka bayan an gama biso, a yayin da akan samu wasu da kan kashe mutane wajen samun sassan jikin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI