Cote d'Ivoire

An ba da belin Kakakin Gbagbo a Ghana

Wata Kotu a kasar Ghana ta bada belin kakakain Tsohon shugaban kasar Cote d’Ivoire, Laurent Gbagbo, wato Justin Kone Katinan, akan bukatar tusa keyarsa zuwa gida domin fuskantar tuhumar cin amanar kasa. 

Tsohon Kakakin Laurent Gbagbo, Justin Koné Katinan
Tsohon Kakakin Laurent Gbagbo, Justin Koné Katinan AFP PHOTO / STR
Talla

An dai kama Katinan ne a watan da ya gabata, bayan Cote d’Ivoire ta bada sammacin duniya dan kamo shi duk inda yake.

An bada belishinsa ne akan kudin Euro 20,000 da kuma kashedin cewa duk makwanni biyu zai dinga kai kansa wajen hukuma.

Lauyoyin Katinan sun tabbatar da cewa Faspo zai cigaba da kasancewa a hanun hukumar tsaron kasar Ghana.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI