Kungiyar Afrika ta AU ta nemi a gudanar da zabe kamin aikawa da dakaru zuwa Mali
Wallafawa ranar:
Kungiyar Kasashen Afrika ta AU, tace shugabanin rikon kwaryar Mali na da karfin da za su iya jagorancin aikin murkushe ‘Yan Tawayen Arewacin kasar, a wani martani na cewa, ya dace a gudanar da zabe kafin a gudanar da aikin sojin. Kwamishinan kula da tsaro, Ramtane Lammara ya sanar da haka a New York, inda yace suna saran, yau a nada Jakada na musamman kan Yankin Sahel, wanda zai kula da aikin.
A shekaran jiya ne, kasar Mali ta nemi da aika da dakaru kasar inda kungiyar kasashen Yammacin Afrika ta ECOWAS ko CEDEAO su ka tabbatar da cewa dakarunta na nan shirye su kutsa cikin kasar ta Mali.
Kasar Faransa ma har ta yi tayin za ta taimaka da bukatun da za su taso na kwato yankin Arewacin kasar da ke hanun ‘Yan tawayen kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu