Zimbabwe
Mugabe ya yi Allah wadai da NATO saboda kifar da gwamnatin Ghaddafi
Shugaban Kasar Zimbabwe, Robert Mugabe, ya zargi kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da mallakar akidar yaki, yayin da yayi Allah wadai da yadda kungiyar NATO ta kifar da gwamnatin shugaba Muammar Ghaddafi a Libya.
Wallafawa ranar:
Talla
Yayin da yake jawabi a Majalisar Dinkin Duniya, shugaba Mugabe, ya zargi kasashen NATO da girman kan da suke ganin cewar sun fi karfin kowa a duniya, inda sukayi watsi da daukacin shirin kungiyar kasashen Afrika na sasanta rikicin Libya.
Sai dai yai kiran kawo karshen yadda manyan kasashen duniya ke yin gaban kansu, wajen murkushe abokan gabansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu