Sudan-Sudan ta Kudu

Sudan da Sudan ta kudu, sun sanya hannu a yarjejeniyar sake fara fitar da mai

Shugabannin kasashen Sudan da Sudan ta kudu, sun sanya hannu a yarjejeniyar sake fara fitar da mai kasuwannin duniya, da kuma samar da tsaro akan iyakokin su. Mai shiga tsakani wajen sasanta rikici, kuma Tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu, Thabo Mbeki, ya bayyana nasarar da suka samu a matsayin gagarumar cigaba.     

Shugaban kasar Sudan, Omar Albashir (hagu) da shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir (dama)
Shugaban kasar Sudan, Omar Albashir (hagu) da shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir (dama)
Talla

A jiya ne dai kasashen Sudan da Sudan ta Kudu, su ka amince da wata yarjejeniyar raba arzikin mai da kuma samar da tsaro kan iyakokin kasashesu, wanda zai ba da damar komawa sayar da mai a kasashen duniya, bayan shugabannin sun kwashe kwanaki hudu suna tattauna a Addis Ababa.

Masu Magana da yawun bangarorin biyu sun ce, shugabannin sun amince da samarwa yankunan tsaro a wasu bangarorin iyakokin kasashen, sai dai taron bai samar da wani cigaba ba akan Yankin Abyei da suke takaddama akai, da kuma wasu sassan iyakokin su.

Yayin da ake ganin wannan yarjejeniya a matsayin cigaba, wasu na kallon ta a matsayin kasa cimma bukatun Majalisar Dinkin Duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI