malawi

Shugabar kasar Malawi ta yadda a rage mata albashi da kashi 30

Shugaban kasar Malawi Joyce Banda
Shugaban kasar Malawi Joyce Banda Reuters / Lefteris Pitarakis

Shugaban kasar Malawi, Joyce Banda, ta ce ta yadda da a rage kashi 30 daga cikin albashinta, a matasyin wani mataki na rage yawan kudaden da ake kashewa a kasar. Haka kuma ragin albashin zai shafi Mataimakin shugabar kasar ta Malawi, Khumbo Kachali.  

Talla

“Saboda mu nuna goyon bayanmu da matakan tsuke aljihun kasarmu, shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa sun yadda a rage musu albashinsu da kashi 30,” inji Kachali.

Shugabar kasar dai na karban akalla Dalar Amurka 5,000 a duk wata amma yanzu za ta dinga karban Dalar Amurka 3,500 ne, a yayin da mataimakinta zai dinga karban Dalar Amurka 2,800 a maimakon Dalar Amurka 4,000.

Tun hawanta kan karagar mulki, a watan Aprilu, Banda na ta daukan matakan ganin cewa ta magance matsalolin da ke addabar tattalin arzikin kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.