Burundi-Tanzania-RFI

Gaskiyar wakilin sashen Swahili na Rfi a Burundi, da aka yankewa hukumcin daurin rai da rai a gidan yari

Hassan Ruvakuki, photographié dans l'enceinte de la prison de Muramvya. RFI
Hassan Ruvakuki, photographié dans l'enceinte de la prison de Muramvya. RFI RFI

Bayan da ya share tsawon watanni 10 a kurkuku, wakilin RFI a Burundi ya bayyana rashin aikata laifin cin amanar kasar da aka zargeshi da yi, a yayinda a ranar 8 ga wannan wata na October ake shirin komawa zaman sauraren shara’arsa da aka daukaka karar, Hasan Ruvakuki ya mikawa wakilan Radio France Intrenationale RFI da suka ziyarce gidan yarin da ake tsare da shi, wata wasika mai taken (Gaskiyata)

Talla

iyalan Hasar Ruvakuki
iyalan Hasar Ruvakuki Jean-Karim Fall

A cikin wasikar Hasan Ruvakiki ya sake jaddada rashin lafinsa, tare da bayyana yadda la murra suka gudana har ta kai ga kotu ta yanke masa hukumcin daurin raid a rai, kan aikata ta’addanci, domin ya zartar da aikinsa na dan jarida.

A wasikar da ya rubuta daga gidan Kurkukun Muramyya, wani gari dake yankin gabashin kasar Burundi, wace ta kunshi gaskiyar lamurra, ba kamar yadda aka zargeshi da zama dan ta’adda ba.

Wasikar da aka mikawa babbar Editar sassan Afrika ta Radiyo Fransa uwargida Anne-Marie Capomaccio, da kuma shugaban sashen Afrika na radiyo France jean Karim Fall, a lokacin wata ziyarar kokarin shawo kan mahukumtan kasar Burundi, tare da wakilan diplomasiyar nahiyar turai a Bujunbura babban birnin kasar ta Brundi, domin nunar da su cewa wakilin radiyon Fransa ya gudanar da aikinsa ne kawai a cikin yanayin siysa mai tsauri.

Aikin rahoto a Tanzaniya

A cikin wasikar mai kunshe da shafuka 3 da ya aikawa RFI, Ruvakuki ya bayyana cewa, bai taba goya wa wata jam’iyar Siysa baya ba, balanta wani gungun masu dauke da makamai, ya kuma zayyana yadda ziyarar tasa ta kasance a tanzaniya har zuwa lokacin da aka kama shi, tare da bayyana yadda ya samu labarin kafuwar kungiyar yan tawayen Burundi a kasar Tanzaniya, kungiyar da ake zargi da kai hare haren ta’addanci da dama a kasar Burundi, dalilin da kuma shine ya sa ya ziyarci kungiyar, domin shirya rahoto ga Radio tashoshin Radiyon Bonesha FM da kuma shashen Swahili na Radiyo Fransa da yake yiwa aiki.

Ravakuki ya ce, kamar duk sauran abukan aiki yan jaridu na duniya, ya tafi ne domin binciken labarin da ya zo masa a matsayin sabo ne. Amma sai aka kama shi tare da zarginsa da aikata laifin ta’addanci, shi da wasu mutane kusan 20.

Shara’a
A lokacin shara’arsa a wata karamar kotu a Bujunbura, lauyoyin wakilin sashen Swahilin na RFI, tare da sauran mutane 13 da aka zargesu tare sun ki cewa uffan saboda zargin taka ka’idodi a wajen gabatar da shara’ar.

Sai dai kuma wata guda bayan faruwar haka, Hasan Ruvakuki da da sauran mutanen 13 an zartar masu da hukumcin daurin rai da rai a gidan yari.

Daga karshen wasikar Hasan Ruvakuki ya rufe da cewa, yau watanni 10 ke nan da yake rufe a gidan yari.
Inda ya ce ta hanyar lauyoyinsa ya na sanar da duniya cewa, baya da laifi, kuma gurin zamansa ba kurkuku yake ba, yana kusa da matarsa ne, da kuma karamar yarsa mai watanni 7 a duniya wace baiga haihuwarta ba, sai kuma sauran abukan aikinsa.

A yayin da wasikar da Hasan Ruvakuki ya aikawa RFI ta kare da wadannan kalamai cewa : « bani da laifi na kuma yi imani da kotu »

Tuni dai kungiyoyin kare hakkin yan jaridu na duniya suka yi ca akan wannan hukumci, wanda suka ce, ya tsananta sosai. Adamu Gorzo shine shugaban kungiyar yan jaridu ta Nahiyar Afrika, wanda ya ziyarci Hasan Ravakuki, ya bayyana cewa, zasu dauki duk matakan da suka dace wajen ganin an sallamoshi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.