Libya

An tsige Prime Ministan kasar Libya

Wata mace na kada kuri'a a Benghazi, yayin zaben 'Yan majalisar Linbya da aka yi a watan Yuli
Wata mace na kada kuri'a a Benghazi, yayin zaben 'Yan majalisar Linbya da aka yi a watan Yuli Reuters/Esam Al-Fetori

MAJLAISAR Kasar Libya, ta kori Prime Minista, Mustafa Abu Shagur, bayan ta ki amincewa da bukatar sa ta nada sabbin ministoci sau biyu.Majalisar dai ta baiwa Abu Shagur wa’adin 72 dan gabatar da sabuwar Majalisar Ministoci, amma kin amincewa da sunayen da ya sake gabatar wa, sai Majalisar ta kore shi, inda Yan Majalisu 125 daga cikin 186 suka kada kuri’ar rashin amincewa da gwamnatin sa.Yanzu Majalisar zata zabi sabon Prime Minista, kamar yadda dokar kasar ya tanada.