Najeriya

Akwai Dan Sanda cikin wadanda suka kai hari a Dogon Dawa

A lokacin da ake binne wadanda suka mutu a harin Dogon Dawa a Kaduna
A lokacin da ake binne wadanda suka mutu a harin Dogon Dawa a Kaduna AllAfrica

Mai Martaba Sarkin Birnin Gwari da ke Jihar kaduna Najeriya, Alh Zubairu Jibril Mai Gwari, ya yi zargin cewa akwai wani Babban jami’in ‘Yan Sanda da ake kira OC, a cikin wadanda suka kai hari Dogon Dawa, inda aka kashe mutane 24.

Talla

A lokacin da Sarkin ke ganawa da ga Gwamnan Jihar, Patrick Yakowa, da shugaban rundunar soji ta daya, da kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Sarkin yace mutanensa ne suka ga jami’in a cikin wadanda suka kai harin, wanda ake zargin kuma ya yi kokarin ganin an saki barayin da ‘Yan bangan suka kama.

Rahotanni dai sun ce, an nemi jami’in ‘Yan Sanda an rasa, domin ya gudu.

Abbas Sarkin Fadan Birnin Gwari, yace an kwashe lokaci ana zargin ‘Yan Boko Haram da aikata kashe kashe a Dogon Dawa amma yace sun gano barayi ne ke addabarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI