Benin

An cafke wadanda ake zargin sun yi yunkurin kashe Shugaban Benin

Shugaban kasar Benin Thomas Boni Yayi kuma shugaban Tarayyar Afrika
Shugaban kasar Benin Thomas Boni Yayi kuma shugaban Tarayyar Afrika © Reuters/Noor Khamis

Mahukuntan kasar Benin sun ce sun cafke Likitan shugaban kasa Thomas Boni Yayi da wani tsohon Minista da ake zargin sun yi kokarin yin amfani da guba domin kashe Shugaban wanda shi ne shugaban kungiyar Tarayyar Afrika.

Talla

Wadanda aka cafke sun hada da tsohon Ministan Masana’antu Moudjaidou Soumanou da likitan Boni Yayi Ibrahim Mama Cisse da kuma wata da ke zaman ‘Yar Shugaban mai suna Zouberath Kora-Seke.

A shekarar 2006 ne Boni Yayi ya karbi shugabancin kasar Benin inda kuma aka sake zabensa a bara.

Ana dai zargin an yi wa Likitan da ‘Yar Boni Yayi alkawalin kudi Biliyan daya na CFA idan har suka yi amfani da kwayu domin kashe shugaban.

Mutumin da kuma ake zargin ya yi alkawalin bayar da kudin shi ne wani attajirin dan kasuwa mai suna Patrice Talonwani tsohon na hannun damar shugaban kafin su samu sabani.

Yanzu haka dai Mista Talon ya fice daga cikin Benin amma mai gabatar da kara Gbenameto ya shiadawa kamfanin Dillacin labaran Faransa za su bayar da sammanin kamo shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI