Najeriya-Rasha

An cafke wani jirgin ruwan Rasha mai dauke da makamai a Najeriya

Wasu Albarussan Bindiga da aka aka kama birnin Kano na Najeriya a wani samame da Jami'an tsaro suka kaddamar bayan kisan mutane 9 a Tudun wada
Wasu Albarussan Bindiga da aka aka kama birnin Kano na Najeriya a wani samame da Jami'an tsaro suka kaddamar bayan kisan mutane 9 a Tudun wada REUTERS/Bala Adamu

Hukumomin Tarayyar Najeriya sun Cafke wani jirgin Ruwan kasar Rasha makare da Bindigogi da Albarusai da suka kai dubu 8,500 da aka yi nufin shiga Najeriya da su ta hanyar mashigin Ruwan Legas da ke kudancin kasar.

Talla

Hukumomin Najeriya sun tsare ‘Yan kasar Rasha 15 da ke janye da Jirgin, inji majiyar Sojin Ruwan kasar.

An dai gano cewar makaman mallakin kamfanin Moran security group ne da ke zaune a birnin Moscow na kasar Russia, amma Kamfanin bai ce komai ba kawo yanzu.

Jirgin na dauke ne da Bindigogi dubu 8, 598 da kuma jibgin Albarusai na Bindigogi daban daban.

Yanzu haka dai ana nan ana bincike akan su, a yayin da wata majiya daga bangaren jami’an Sojin Ruwa na Tarayyar Najeriyar ta tabbatar da cewa daga ciki akwai wasu makamai masu sarrafa kansu.

Bincike dai ya nuna cewa shiga da makamai ya kasance babbar Sana’a ga wasu bata-gari a Najeriya, kasar da yanzu haka ke fama da fashe-fashen Boma Bomai da fashi da makami, da kuma garkuwa da mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI