Rwanda-Congo-Uganda

An sake zargin Rwanda da Uganda suna taimakawa ‘Yan tawayen Congo

Wasu 'yan tawayen M23 na Jamahuriyar democradiyyar Congo a lokacin da suke ficewa birnin Goma
Wasu 'yan tawayen M23 na Jamahuriyar democradiyyar Congo a lokacin da suke ficewa birnin Goma Reuters

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya sake zargin kasashen Rwanda da Uganda suna taimakawa ‘Yan tawayen Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo a ta’asar da suke yi a gabashin Congo.

Talla

Rahoton wanda wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya rubuta ya aika wa Kwamitin sulhu cewar ‘Yan tawayen na Congo da ake kira M23 sun sami gudunmawa daga kasar Rwanda da Uganda wajen karbe ikon garin Goma.

Bayanan masana na cewa ko shakka babu kasashen biyu sun taka gagarumar rawa wajen aika-aikan da aka yi a kasar Congo.

Kasar Rwanda da Uganda dai sun sha musanta cewa ko kadan babu hannunsu cikin rikicin da ake ta tafkawa tun farkon watan jiya.

Da farko dai dakarun kasar Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ne suka kai harin da ya kashe ‘yan tawaye sama da 40 da suka hada da wasu Sojan Rwanda a kan iyakan kasashen, kamar yadda rahoton ke nunawa.

Majiyoyi sun gaskata cewa a lokacin da ‘yan tawayen M23 suka doshi zuwa garin Goma ne kuma sai Dakarun Rwanda suka rufa masu baya kafin su fice daga garin a jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.