Masar

An tare ‘Yan adawan Masar daga isa fadar shugaba Mursi

Sojojin Masar sun datse hanyar isa fadar Shugaba Mursi
Sojojin Masar sun datse hanyar isa fadar Shugaba Mursi Reuters/路透社

Dakarun kasar Masar sun yi arangama da ‘Yan tawaye, wandanda ke kokarin shiga fadar Shugaban, bayan wannan rikici da ya samo asali bayan fadada iko da Shugaba Mohammed Mursi ya yiwa kansa makwanni biyu da suka gabata.

Talla

Rahotannin daga Masar na nuna cewa dakarun kasar, sun sanya wani shinge na waya tare da tankunan yaki, wanda tazararsa daga fadar ya kai tsawon mita 150, bayan an umurci ‘Yan adawar da su janye.

A garin Zagazig, wanda daga nan Morsi ya fito, ‘Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye, wajen tarwatsa wasu masu zanga zanga da suka mamaye gidan wani dan uwan shugaba Morsi.

Wata majiya mai karfi ta fadawa Kamfanin Dillancin labari na AFP cewa, akalla mutane bakwai suka mutu a yayin da sama da 600 suka jikkata tun bayan barkewar rikicin tsakanin magoya bayan Morsi da ‘Yan adawa, tun bayan ikon da shugaba Morsi ya fadadwa kansa.

An dai nemi magoya bayan Shugaba Morsi ma su janye daga sansanin da suka kafa, a yayin da wasu daruruwan ‘Yan adawa suka make a kusa da fadar.

Sai dai shugaban dakarun da aka jibge a kofar fadar, Janar Mohammed zaki, yace tankunan yakin da aka kawo wurin, za a yi amfani da sune domin raba fada tsakanin magoya bayan Morsi da ‘Yan adawa.

Sai dai duk da zanga zangar da ake yi Shugaban na Masar ya ce za a gudanar da jefa kuri’ar jin ra’ayin a ranar 15 ga watan nan, a dai dai lokacin da shugaban ‘Yan adawa Mohammed El- Baredie ke zargin Mursi da haddasa wannan rikici.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.