Isa ga babban shafi
Faransa-Algeria

Hollande ya isa Algeria domin dinke barakar da ke tsakaninsu da Faransa

Shugaban kasar Faransa François Hollande
Shugaban kasar Faransa François Hollande Reuters
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
1 min

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya kai ziyarar kwanaki biyu a kasar Algeria domin farfado da dangantar da ke tsakanin kasar da Faransa tare da inganta huldar kasuwanci. Wannan ce ziyara ta farko da Hollande ya kai a Algeria bayan ya gaji Nicolas Sarkozy a  lokacin da kasar ta gudanar da bukin cika shekaru 50 da samun ‘yancin kai daga Faransa.

Talla

Francois Hollande zai gana da shugaba Abdelaziz Bouteflika kuma batutuwan da zasu tattauna sun hada da neman goyon bayan mahukuntan kasar Algeria su amince da daukar matakn soji a kasar Mali.

A watan Oktoba Shugaba Hollande ya amince da kisan gillar da ‘yan sandan Faransa suka yi wa al’ummar Algeria masu zanga-zangar neman ‘yanci a birnin Paris a shekarar 1961, inda masana tarihi suka ce daruruwan mutane ne suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.