Mauritania

Jagoran ‘Yan adawa a Muaritania ya yi gargadin tura dakarun kasar zuwa Mali

Dakarun Hadin Gwiwa na Kungiyar ECOWAS
Dakarun Hadin Gwiwa na Kungiyar ECOWAS dailynewsegypt.com

Jagoran ‘Yan adawa a kasar Mauritania, Ahmed Ould Daddah, ya gargadin Hukumomin kasar da kada su tura sojan kasar cikin na kasashen kungiyar kawance dake shirin hada kan sojan da zasu farma yankinArewacin kasar Mali, inda masu kishin Islama suka kwace.

Talla

A cewar Daddah a lokacin da yake ganawa da manema labarai, ko kadan batun an Mali bai shafesu ba, saboda haka kada kasar ta shiga.

A jiya kungiyar kasashen Afrika suka kara nuna bukatar a hanzarta kubutar da Arewacin Mali daga hannun ‘Yan tawayen.

Kungiyar kasashen yammacin Africa dai na da Dakaru 3,300 da zasu tura wannan aiki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.