Mali-MDD

Kwamitin tsaro na MDD ya amince da bukatar daukar matakin Soji a Mali

Mayakan Kungiyar Ansar Dine,  a Mali.
Mayakan Kungiyar Ansar Dine, a Mali. REUTERS/Adama Diarra

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da bukatar kasashen Afrika na tura dakarun Soji zuwa Mali domin karbe ikon Arewacin kasar da ya fada hannun ‘Yan tawaye tun a Watan Maris da Sojoji suka hambarar da Gwamnatin Amadou Toumani Toure.

Talla

Dafrin wanda kasar Faransa ta gabatar ya kuma amince kasashen Turai da Majalisar Dinkin Duniya su taimaka wajen daidaita tsaro a kasar Mali.

Sai dai Kwamitin tsaron wanda ke da mambobi 15, ya bayyana cewa, yin amfani da karfin soji, zai zo daga baya idan har wasu hanyoyin sasantawa ta fuskar siyasa sun gagara

Wannan kuma na zuwa ne a dai dai lokacin da wani rahoto na Hukumar kare hakkin Bil adama ta Human Rights Watch ke cewa, ana samun ramukon gayya akan Fararen hula ‘Yan kabilar Abzinawa saboda tawayen da wasu ‘Yan kabilar ke yi.

Tuni dai kasashen kungiyar Yammacin Afrika ta ECOWAS ta bayyana shirin aikwa da dakaru 3,300 a Mali.

Bayan Mayakan Ansar Dine da ‘Yan tawayen Abzinawa sun karbe ikon Mali bangarorin biyu sun samu rashin jituwa a tsakaninsu inda Ansar Dine suka ce lalle sai sun girka Shari’ar Musulunci wanda kuma ya sabawa ‘Yan tawayen Abzinawa.

Yanzu haka kuma birnin Timbuktu mai dinbim tarihi a Mali yana hannun Mayakan Ansar Dine

Rikicin kasar Mali

Dubban mutanen Mali ne dai suka yi gudun hijira daga arewaci zuwa makwabtan kasashe.

Wani Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya yi hasashen cewar mutane sama da 400,000 za’a raba da gidajensu idan har aka kaddamar da yaki ‘Yan tawaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.