Najeriya

‘Yan Bindiga sun cinna wa Coci wuta tare da bindige mutane 6 a Najeriya

Fafaroma Benedict a Fadar Vatican lokacin da ya ke mika sakon Kirsimeti ga Mabiya kirista a Fadin Duniya tare da kiran kawo karshen zubar da jini a Najeriya
Fafaroma Benedict a Fadar Vatican lokacin da ya ke mika sakon Kirsimeti ga Mabiya kirista a Fadin Duniya tare da kiran kawo karshen zubar da jini a Najeriya REUTERS/Alessandro Bianchi

Wasu ‘Yan bindiga sun bude wa Mabiya Addini kirista wuta a wata Mujami’a da ke garin Peri kusa da Potiskum a Jahar Yobe Arewacin Najeriya inda suka kashe mutane Shida tare da cinnawa Mujami’ar wuta a ranar Jajibirin Kirsimeti.

Talla

Wannan harin na zuwa ne a dai dai lokacin da Fafaroma daga Fadar Vatican ke kiran kawo karshen zubar da jini a Najeriya da sauran kasashen Duniya masu fama da tashe tashen hankula.

Wani Mazauni garin kauyen Peri Usman Mansir, ya shaidawa AFP cewar ‘Yan bindigar sun kai harin ne a tsakiyar dare lokacin da Mabiya Kirista ke ibada inda suka bude wuta suka kashe Pastor da wasu mabiya Biyar a Mujami’ar.

Rundunar ‘Yan Sandan Jahar Yobe dai ta tabbatar da faruwar lamarin kodayake babu wani karin haske daga Kwamishinan ‘Yan sandan Jahar, Sanusi Rufa'I.

A bara dai an taba kai hari a ranar Kirsemeti inda mutane 44 suka mutu a Arewacin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.