Afrika ta Tsakiya

‘Yan tawayen Afrika ta Tsakiya sun isa Gabon domin tattaunawa da Gwamnati

Wakilan 'Yan tawayen Seleka akan hanyarsu daga Ndjamena zuwa Libreville.
Wakilan 'Yan tawayen Seleka akan hanyarsu daga Ndjamena zuwa Libreville. RFI/Sara Sakho

Shugabannin ‘Yan tawayen Afrika ta Tsakiya da suka karbe manyan biranen kasar sun isa kasar Gabon domin tattaunawa da Gwamnati a birnin Libreville don kawo karshen rikicin da ya gurgunta kasar.

Talla

Tuni dai shugaban kasar Afrika ta tsakiya Francois Bozize ya gana da takwaransa na Congo Denis Sassou Nguesso, wanda ke aikin shiga tsakanin rikicin kasar da ‘Yan tawaye.

Mambobin ‘Yan tawayen 15 ne suka kai ziyara Gabon a cikin wani jirgin saman Majalisar Dinkin Duniya.

Shugaban ‘Yan tawayen na Seleka Michel Djotodia, ya shaidawa AFP cewa “ Mutum ba zai shiga yaki ba, ba tare da neman hanyoyin samun zaman Lafiya ba”.

A lokacin da ya ke ganawa da manema labarai Shugaban Congo Sassou Nguesso yace daukar matakin Soji ba zai kasance hanyar kawo karshen rikicin kasar ba.

Mista Bozeze dai ya bayyana fatar samun daidaito tsakaninsu da ‘Yan atwaye domin samun zaman lafiya a Afrika ta Tsakiya.

Amma ‘Yan tawayen kasar  sun jajirce dole sai Bozeze ya yi murabus wanda ke saman mulki tun a shekarar 2003 kafin su amince da tattaunawar. Sai dai Shugaban Congo yace zai nemi ‘Yan tawayen su sauya matsayinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.