Algeria-Mali

Kasashen duniya sun daura laifin kisan ‘yan kasashen waje akan ‘yan tawyen Algeria

Kamfanin tace gas na Amenas dake Algeria, inda anan ne aka yi garkuwa da mutanen.
Kamfanin tace gas na Amenas dake Algeria, inda anan ne aka yi garkuwa da mutanen. REUTERS/Kjetil Alsvik

Kasashen duniya sun dora laifin zubar da jinin da aka yi, yayin kwato mutanen da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a cibiyar aikin gas din kasar Algeria, kan masu garkuwan, maimakon matsayin da suka dauka a baya, na dora laifin kan hukumomin kasar. Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius, da maharan suka ce shigar kasar shi yaki a Mali ya sa suka kai harin, ya bayyana kaduwa kan yadda aka dora alhakin lamarin kan kasar Aljeriya. 

Talla

Fabius ya ce bai kamata a bar ‘yan ta’adda suna cin karen su ba babbaka ba, duk da cewa kowa na fatan ganin an karya lagon ‘yan bindigan, don a ceto mutanen da aka yi garkuwar da su.
 

Fadar PM kasar Britaniya David Cameron tace, mutane na tambaya kan yadda hukumomin kasar Algerian suka yi gaban kan su wajen daukar matakai, amma a cewar fadar, alhakin mutuwa mutanen na kan ‘yan ta’addan da suka kai harin.
 

A ranar alhamis dakarun kasar aljeriya suka far wa cibiyar aikin Gas din, da nufin ceto daruruwan mutanen da suka hada da ma’aikata ‘yan kasashen waje kusan 100, da ‘yan bindigan suka yi garkuwa da su, inda ake tunani a wadanda aka yi garkuwa da su 25, da kuma ‘yan bindiga 32 sun rasa ran su.
 

A halin da ake ciki kuma, Sojojin Algeria sun ce, sun sami 5, daga cikin masu garkuwan, yayin da 3 suka tsere.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI