Janhuriyar Afrika ta Tsakiya

‘Yan tawayen Afrika ta Tsakiya sun amince da bukatar Bozize ta nadin mukamai

Shugaban kasar Janhuriyar Afrika ta Tsakiya, Francois Bozize
Shugaban kasar Janhuriyar Afrika ta Tsakiya, Francois Bozize AFP PHOTO/JOHN THYS

Bayan nuna rishin amincewarsu da shirin Shugaban kasar Janhuriyar Afrika ta Tsakiya Francois Bozize na nada wadansu daga cikin mambobin kungiyar ‘Yan tawayen Seleka, Kakakinsu, Janar Mohamed Moussa Dhaffane, a wata sanarwa ya ce sunyi na’am da bukatar Shugaban kasar Francois Bozize.

Talla

A cewar Dhaffane, ko kadan bamu da niyar kin amsa shiga sabuwar Gwamnatin Shugaban Bozize duk da cewar a taron sassanta ‘yan tawayen, a kasar gabon akwai sharuda da ya kamata ita gwamnatin ta bi.

Ya kara da cewa, kusan da cewar rashin yin hakkan ya sa ya kawo jan kaffa daga bangaren, ‘Yan tawayen.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.