Tunsia

Tunisia ta shiga rudanin Siyasa bayan kisan Madugun Adawa

Daruruwan Masu Zanga-zanga a harabar Majalisar Tunisia dauke da hoton Shugaban Adawa Chokri Belaid
Daruruwan Masu Zanga-zanga a harabar Majalisar Tunisia dauke da hoton Shugaban Adawa Chokri Belaid REUTERS/Anis Mili

Jam’iyya Shugaban kasar Tunisia, Moncef Marzouki, ta yi amai ta lashe, kan matsayinta na ficewa daga cikin Gwamnati hadaka, Amma ta tsaya kan matsayin lalle sai Ministocin Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi ta Ennahda sun yi murabus saboda kisan da aka yi wa shugaban ‘Yan adawa, Chokri Belaid.

Talla

Shugaban Jam’iyar, Mohammed Abbou yace sun ba Gwamnati nan da mako guda domin sauya al’amurra in ba haka ba za su fice daga Gwamnatin hadaka.

Jam’iyyar ta CPR ta bukaci Ministan Shari’a da Firaminista Hamadi Jebali na Ennahda su yi murabus saboda kwantar da wutar rikicin kasar bayan kashe Chokri Belaid.

An kwashe kwanaki uku ana zanga-zanga a kasar Tunisia bayan kisan madugun ‘Yan adawar, al’amarin da ya yi sanadiyar mutuwar Dan sanda da raunata wasu 59.

Dubban masu zanga-zanga ne suka kewaye harabar Majalisar kasar suna masu bukatar lalle sai shugabannin Gwamnatin sun yi murabus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.