Najeriya

An karbi Belin ‘Yan Jaridun da aka kama game da Polio a Najeriya

Allurar Rigakafin Cutar shan-inna da ake diga wa Yara
Allurar Rigakafin Cutar shan-inna da ake diga wa Yara /www.unicef.fr

An bayar da Belin wasu ‘Yan jaridu Biyu da Gwamnatin Jihar Kano a Arewacin Najeriya ta gurfanara Kotu, bisa zargin tunzura al’umma, domin kyamatar allurar rigakafin cutar shan inna (Polio) da ake yi wa yara a Jahar.

Talla

A ranar 8 ga watan Fabrairu wasu ‘Yan bindiga suka kashe wasu Jami’an kiwon lafiya masu diga ruwan maganin Polio su 10 bayan kafar yada labaran Wazobia FM ta yada labarin tursasawa mutane su amince da Allurar.

Daya daga cikin ‘Yan jaridar ya ce ya sha duka tare da karbe masa kayan aiki a harabar gidan wani malami Abubakar Rabo da jami’an kiyon lafiyar suke kokarin tursasa ma shi ya amince su diga wa yaran shi maganin Polio.

An karbi Belin ‘Yan jaridun ne akan kudi Naira Dubu Dari.

Adamu Gwarzo shugaban kungiyar ‘Yan jaridu ta Nahiyar Afrika yace Lauyan kungiyarsu Sa’idu Muhammad ne ya tsaya wa ‘Yan jaridar a gaban Kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.