Masar

An saka ranar sake yiwa Hosni Mubarak sabuwar shari’a

Tsohon shugaban kasar Masar, Hosni Mubarak a loakcin da ya ke tsare bayan an yanke mai hukuncin daurin rai da rai
Tsohon shugaban kasar Masar, Hosni Mubarak a loakcin da ya ke tsare bayan an yanke mai hukuncin daurin rai da rai 路透社

Hukumomin Kasar Masar sun ce za’a sake yiwa Tsohon shugaban kasar, Hosni Mubarak shari’a daga ranar 13 ga watan gobe, saboda zargin da ake masa na hannu wajen kashe masu zanga zanga.

Talla

Wata kotun daukaka kara ta soke daurin rai da ran da aka masa, ta kuma bada umurnin sake shari’ar ta sa, tare da wasu jami’ansa, da suka hada da tsohon ministan cikin gida, Habib al-Adly da wasu manyan jami’an tsaro shida.

An dai yankewa Mubarak da Adly hukuncin kisa ne a ranar 2 ga watan Yunin bara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.