Isa ga babban shafi
Duniya

Kwararru sun yi gargadin yiwuwar gushewar Giwaye daga doron kasa

Giwaye dauke da haurukansu
Giwaye dauke da haurukansu
Zubin rubutu: Mahmud Lalo
Minti 1

Kwararru a fannin kula da namun daji sun yi gargadin yiwuwar gushewar giwaye daga doron kasa muddin aka ci gaba da kasuwancin sayar da haurensu a duniya. Wannan gargadi na zuwa ne a dai dai lokacin da kashe giwayen saboda cire haurensu ya kazanta a kasashen dake da yawan giwa a dazukansu duk da cewa an haramta yin hakan shekaru aru-aru da suka gabata. 

Talla

Yawan gungun masu farautar hauren giwayen ya karu da ninki biyu tun daga shekarar 2007 ya kuma kara ninkuwa sau uku a shekaru 15 da suka gabata, inda kwararrun suka yi gargadin cewa giwaye na cikin hadari a doron kasa.

Batun sayar da hauren giwaye da na dorinar ruwa sun kasance muhimman batutuwa da aka tattauana a wani taron kungiyoyin dake kare namun dajin da ke fuskantar barazanar gushewa daga doron kasa inda taron ya samu halartar mambobi 178 a birnin Thai dake Thailand.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.