Jamhuriyyar Congo

Gwamnatin Congo ta yi tayin za ta yi wa ‘Yan tawayen M23 afuwa

Shugaban 'Yan tawayen M23, Bertrand Bissimwa.
Shugaban 'Yan tawayen M23, Bertrand Bissimwa. Photo AFP / Isaac Kasamani

Gwamnatin Kasar Congo ta ce za ta yi Afuwa ga ‘Yan Tawayen kasar, tare da alkawalin sanya su cikin rundunar sojin ta, muddin suka amince su aje makaman su a cikin wanna mako.

Talla

Ministan yada labaran kasar, Lambert Mende yace za’a kamamla tattaunawa da ‘Yan Tawayen ranar 15 ga wata, kuma za’a aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla.

Amma a bangare daya, ‘Yan Tawayen sun ce ba su da wata masiniya game da wata tattaunawa da ake gudanar wa, kamar yadda kakakin su Kanal Seraphin Mirindi ya bayyana, tare da gargadin ci gaba da yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.