Tunisia

Wani Mutum Mai sayar da Sigari ya cinnawa kansa wuta a Tunisia

Abdel Khadir mai sayar da taba Sigari Wanda ya cinnawa kansa wuta a tsakiyar Birnin Tunis na kasar Tunisia
Abdel Khadir mai sayar da taba Sigari Wanda ya cinnawa kansa wuta a tsakiyar Birnin Tunis na kasar Tunisia REUTERS/Stringer

Wani dan kasuwa mai sayar da Taba Sigari ya cinnawa kansa wuta a tsakiyar birnin Tunis domin fusata da tsadar rayuwa. Rahotanni sun ce mutumin ya fita hayyacin shi amma an kwashe shi zuwa Asibiti.

Talla

Wannan na zuwa ne sa’oi kafin Majalisar kasar ta kada kuri’ar zaben sabuwar gwamnati.

Mahukuntan kasar sun bayyana mutumin da sunan Adel Khadri dan shekaru 27 wanda ya fito daga gidan wasu karamin karfi a Jendouba yankin arewa maso yammacin kasar.

Wadanda abun ya faru a gaban idonsu sun ce, sai da Adel Khadri ya fasa ihu kafin ya cinnawa kansa wuta a harabar ginin majalisa.

Irin wannan ne dai ya haifar zanga-zanga a kasar Tunisia da har ya yi sanadiyar hambarar da gwamnatin Zine El Abidine Ben Ali bayan wani mai suna Habib Bourguiba ya cinnawa kansa wuta saboda tsadar ruyuwa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.