Sudan

Al Bashir zai kai ziyara kudancin Sudan

Shugaban kasar Sudan Umar Hassan al Bashir ya amsa goron gayyatar zuwa Kudancin Sudan bayan kasashen biyu sun amince su koma teburin sasantawa game da yankunan masu arzikin man fetir da ke kan iyakakin kasashen biyu.

Shugaban kudancin Sudan Salva Kiir (dama) da Shugaban Sudan Omar al-Bashir  tare da Thabo Mbeki
Shugaban kudancin Sudan Salva Kiir (dama) da Shugaban Sudan Omar al-Bashir tare da Thabo Mbeki Reuters/Tiksa Negeri
Talla

A wata sanarwa daga Fadar shugaba al Bashir, kakakinsa Emad Sayed Ahmed yace shugaban ya amince ya kai ziyara kudancin Sudan bayan shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu ya tuntubi shi ta wayar salula.

Sai dai babu wata rana da aka ware domin ziyarar ta al Bashir.

Shugabar hukumar Tarayyar Afrika Nkosazana Dlamini-Zuma tace suna fatar ziyarar al Bashir ta kasance hanyar kawo karshen rikicin da ke tsakanin kasashen biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI