Afrika ta Kudu

Nelson Mandela na cigaba da samun sauki, bayan an kwashe shi zuwa Asibiti

Tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu, Nelson Mandela
Tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu, Nelson Mandela Reuters

Gwamnatin kasar Afrika ta Kudu tace tsohon Shugaban kasar Nelson Mandela yana samun sauki duk da ya kwashe kwanaki uku ke nan a Asibiti saboda rashin lafiyar Huhu. Tun da aka kwashi Mandela zuwa Asibiti ne Shugabanni duniya ke ta aiko da sako fatar alheri ga tsohon Shugaban, kuma kakakin gwamnatin Jabo Zuma, Mac Maharaj yace Mandela ya tashi da safe tare yin Karin kumallo. 

Talla

Zuma yace Mandela ya samu sauki sosai harma ya yi karin kumallon safe a yau Jumu’a, sai dai ana cigaba da bashi Magani, yana kuma samun kulawar Likitoci a kasar ta Afruka ta kudu.

Gwamnatin kasar ta yi kira ga al’ummar kasar su yi wa shugaban addu’a domin samun sauki.
Sanarwar Rashin lafiyar shugaban ta fito ne daga fadar shugaba Jacob Zuma inda aka bayyana cewa an kwashi Mandela ne zuwa asibiti da tsakiyar daren Laraba.
Wannan ne kuma karo na biyu da aka kwash Mandela zuwa Asibiti a tsakiyar dare bayan ya kwashe tsawon makwanni uku a watan Disemba saboda rashin lafiyar huhu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.