Afrika ta Kudu

Iyalan Mandela sun ziyarce shi a asibiti

Nelson Mandela tare da Albertina Sisulu
Nelson Mandela tare da Albertina Sisulu © Reuters

A tsakiyar ranar yau litinin wata tawaga da ta kunshi iyalan tsohon shugaban kasar ta Afirka ta kudu Nelson Mandela ta kai masa ziyara a asibitin da yake jinya, wato kwanani da dama bayan an kawantar da shi sakakamakon rashin lafiyar da yake fama da shi.

Talla

A wata sanarwa da likitocin Mandela suka fitar a tsakiyar ranar ta yau, sun bayyana cewa daga jiya zuwa yau ba wani sauyin da aka sama a game da lafiyar tsohon shugaban dan kimanin shekaru 94 a duniya to amma dai zai ci gaba da kasancewa a asibiti.
A sanarwar da suka fitar a jiya kuwa, likittocin sun ce Nelson Mandela na iya yin numfashi da kansa, sabanin yadda a can baya sai an taimaka masa da wasu na’urori domin yin numfashin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI