Mali

Dakarun Turai sun fara horar da takwarorinsu na Mali

Dakarun Mali
Dakarun Mali France24 / capture d'écran

Dakarun kasashen Turai sun fara ba dakarun Mali horo a yau Talata a sannin Kulikoro da ke kusa da birnina Bamako. Dakarun na Mali zasu samu horo ne domin tafiyar da tsaro tare da kare iyakokin kasar Mali.  

Talla

Laftanar Kanar Yacouba Sanogo, daya daga cikin masu karbar horo, yana mai fatar samun gamsasshen horo daga dakarun na Turai.

Sai dai a garin Timbuktu, rahotanni sun ce an ci gaba da gwabzawa tsakanin dakarun Mali da ‘Yan tawaye.

Mutane uku aka kashe a jiya Litinin wanda hakan ya kai adadin wadanda aka kashe zuwa 11 tun fara musayar wutar a ranar Asabar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI