Afrika ta Kudu

'Yan adawar Afirka ta Kudu sun nemi janye sojan kasar daga Afirka ta Tsakiya

Jacob Zuma, Shugaban Afirka ta Kudu
Jacob Zuma, Shugaban Afirka ta Kudu REUTERS/Rogan Ward

Babbar jam’iyyar adawar kasar Afrika ta Kudu AD, ta bayyana aniyarta ta shigar da wata bukata a gaban ‘yan majalisar dokokin kasar, domin tilastawa gwamnati wajen ganin ta sake maido da sojojin kasar da ta tura a Jamhuriyar Afrika ta Tsakkiya ba tare da bata lokaci ba.

Talla

Daukar wannan mataki da jam’iyyar take neman a yi, ya biyo bayan mutuwar dakarun kasar 13 ne a kasar ta Afrika ta tsakkiya lokacin da ‘yan tawaye ke kokarin kutsawa birnin Bangui domin kifar da gwamnatin Francois Bozize.

Wannan dai shi ne hasarar dakaru soja, mafi girma da kasar ta Afrika ta kudu ta taba fuskanta, tun bayan kawo karshen mulkin nuna wariyar launin fatar kasar a 1994.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.