Guinea Bissau-Amruka

Amruka ta kama tsohon shugaban rundunar sojin ruwan Guinea Bissau, Rear Admiral Bubo Na Tchuto...

Rear Admiral Bubo Na Tchuto
Rear Admiral Bubo Na Tchuto allvoices.com

Hukumomin Tsaron Amurka sun yi nasara kama tsohon shugaban rundunar sojin ruwan Guinea Bissau, Rear Admiral Bubo Na Tchuto, wanda ake nema ruwa ajallo saboda zargin hannu wajen safarar miyagun kwayoyi.An dai kama jami’in ne tare da wasu mutane hudu a cikin wani jirgin ruwa, inda aka tafi da shi zuwa Cape Verde, akan hanyar kai shi Amurka.Jami’in ya taka rawa wajen juyin mulkin da dama a kasar ta Guinea Bissau.