Cote d'Ivoire

za a binne gawarwakin kimanin mutane 3.000 da aka kashe a rikicin siyasar kasar cote dIvoire da ya gabata

ana tsamo wasu  gawarwakin mutane da aka gano a wata  rijiya a garin  Duékoué.
ana tsamo wasu gawarwakin mutane da aka gano a wata rijiya a garin Duékoué. Amnesty International

Hukumomin Kasar Cote d’Ivoire sun kadadmar da shirin tona kaburburan mutanen kasar sama da 3,000 da aka kashe sakamakon tashin hankalin zabe, da gudanar musu da jana’iza ta musamman.Ministan shari’ar kasar, Gnenema Coulibaly, yace ya zuwa yanzu gawawakin wadanda aka kashe na warwatse a wuraren jama’a 57 da suka hada da wuraren ibada, gidaje da asibitoci, saboda haka ya dace a tono su dan yi musu jana’izar da ta dace.Kasar Cote d’Ivoire dai ta yi fama da yaki ne sakamakon nuna turjiyar da tsohon shugaban kasar Laurent Bagbo yayi ya ki sauka daga kan madafan iko duk da cewa ya fadi a zaben shugabancin kasar.