Afrika ta Kudu

An sake sallamar Mandela daga Gadon Assibiti

Nelson Mandela tare da Matar sa Winnie, a shekarar 1990.
Nelson Mandela tare da Matar sa Winnie, a shekarar 1990. Allan Tannenbaum

Ofishin shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma, ya tabbatar da sallamar tsohon shugaban kasar Afrika Mr Nelson Mandela daga Assibiti, bayanda yayi jinyar cutar Mura mai tsanani har ta tsawon kwanaki Goma a Assibiti, Nelson Mandela dai sananne ne kan Yaki da nuna banbancin wariyar launin Fata a kasar dama Duniya baki daya

Talla

Mai Magana da Yawun shugaban kasar Afrika ta kudu ya bayyana wa Duniya cewar sallamar da aka yiwa Mandela ta biyo ne bayan lura da yanda halin Lafiyarsa ke dada kyautatuwa.

Kamar wancan lokacin da yayi jinya tsohon shugaba Mandela zai cigaba ne da karbar Magani a Gida.

Wannan dai shine karo na Ukku da aka kwantar da Mandela a Assibiti kama daga Watan Disamban Baara.

A Watan da ya gabata dai an kwantar da Mandela ne na tsawon kwana daya, akan bukatar rinka duba lafiyar sa lokaci-lokaci, aka kuma sake kwantar da shi a cikin Watan Disamba na tsawon kwanaki Goma sha Takwas akan matsalar Huhu.

Shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma ya mika sakon godiya ga al’ummar kasar dama na Duniya baki-daya akan fatan alkhairi da suke yiwa Dattijo nelson Mandela.

Ya kuma godewa Likitocin kasar da sukayi aiki babu kama Hannun Yaro, domin ganin sun dakushe cututtukan da Mandela dan shekara 94 yake fama da su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI