Africa ta Kudu

Wani mutum yayi nasarar tsallaka Teku da Ballon-ballon daga Kurkukun Mandela zuwa Cape town

Mai kasadar hawan Ballon-ballon a Afrika ta kudu
Mai kasadar hawan Ballon-ballon a Afrika ta kudu

Wani mutum dan asalin kasar Afrika ta kudu yayi nasarar tsallaka Teku daga kurkukun da Mandela yayi zaman jarin zuwa birnin Cape town na kasar ta Afruka ta kudu, yana mai bayyana nasarar da ya samu da cewar sam bata kama Kafar irin wadda tsohon shugaban kasar Mr Nelson Mandela ya samu ba.  

Talla

Wannan mutumin dai yayi wannan kasadar ne ta tafiya akan Teku har tsawon Kilomita shida da manufar tattara kudaden tallafi ga Assibitin kula da kananan Yara da aka yiwa suna da tsohon shugaban kasar Mr Nelson Mandela.

Mutumin dan shekara 37 mai suna Matt Silver-Vallance,  ya share kusan Awa daya yana tafiya makale a karkashen dandazon Balon-balon da aka cika da Iska ya kuma ratsa Tekun Atlantika daga tsibirin Robben Island zuwa Cape town.

A lokacin da ya sauka lafiya sai yayi kururuwa yana bayyana hakan a matsayin babbar Kasadr da yayi, kuma bai yi tsammanin zai kai labari ba, sai dai yayi kashedin cewar kar wani ya gwada hakan a gaba.

Akalla dai Silver-Vallance ya cika Ballon-ballon 35 ne a wannan Tafiya mai kasada da yayi.

Silver yace zasu yi amfani da wannan damar domin tattara kudade ga Assibitin kananan Yara ta Nelson Mandela wadda na dai daga cikin abin azo-a-gani da Mandela yayi a Rayuwar sa, kuma a cewar sa, hawan Ballon-ballon da yayi ba wani abu ba ne idan aka lura da abubuwan da Dattijo Mandela yayi a Rayuwar sa.

Yace Kasadar da yayi ta hawan Ballon-ballon bata kai wadda Mandela ya runguma ba, domin ganin bayan wariyar launin Fata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI