Mali-Faransa-Chadi

Dan kunar bakin wake ya kashe sojan Chadi uku a Mali

Ayarin sojan Chadi a kasar Mali
Ayarin sojan Chadi a kasar Mali AFP / Sia Kambou

Akalla sojojin kasar Chadi 3 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kai a sanyin safiyar yau a birnin Kidal na arewacin Mali.

Talla

Wata majiyar sojan kasar ta Chadi ta tabbatar da faruwar wannan lamari, inda ta ce wani mutum ne da ya yi jigida da manyan bama-bamai ya tarwatsa kansa bayan da kutsa a cikin gungun sojojin kasar ta Chadi, kuma ko baya ga wadanda suka rasa rayukansu akwai wasu sojoji akalla hudu da suka samu raunukaa lokacin da wannan lamari ya faru.
Kawo yanzu dai sojojin Chadi 30 ne aka tabbatar da cewa sun rasa rayukansu tun daga lokacin da suka shiga Mali domin taimaka wa sojojin Faransa don yakar ‘yan tawaye da ke mamaye da arewacin kasar ta Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI