Sudan-Sudan ta Kudu

Shugaba El-bashir na ziyarar farko a Sudan ta Kudu

El-bashir na Sudan da Silva Kir na Sudan ta Kudu
El-bashir na Sudan da Silva Kir na Sudan ta Kudu

Shugaban kasar Sudan Umar Hasan Al-bashir wanda ke gudanar da ziyarar aiki ta farko a makwabciyar kasarsa wato Sudan ta Kudu a yau juma’a, ya ce babbar fatarsa ita ce samar da kyakkyawar alaka tsakanin kasashen biyu.

Talla

Kasashen biyu dai sun amince da wata yarjejeniyar sullhu ce a tsakaninsu a cikin watan maris da ya gabata wadda ta bayar da damar ci gaba da yin jigilar man fetur na Sudan ta Kudu zuwa gabar ruwa ta hanyar yin amfani da bututun mai na kasar Sudan.
A shekara ta 2011 ne aka kafa kasar Sudan ta Kudu kamar dai yadda yarjejeniyar sulhun da ta kawo karshen yakin basasar tsawon shekaru 25 a tsakanin al’ummar sabuwar kasar da kuma gwamnatin birnin Khartum ta tanada.
A cikin shekarar bara ne dai ya kamata Umar Albashir ya ziyarci birnin Juba na Sudan ta Kudu to amma sai wani rikici ya barke a yankin da ake kira da suna Abyei mai dimbin arzikin man fetur wanda kasashen biyu ke takaddama a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI