Somaliya

Asusun Lamuni na Duniya zai yi aiki da gwamnatin Somaliya

Hassan Sheikh Mohamud, shugaban Somaliya
Hassan Sheikh Mohamud, shugaban Somaliya Reuters/Tiksa Negeri

Asusun Lamuni na Duniya IMF, ya amince da gwamnatin da aka kafa a Somaliya a matsayin karbabbiyar gwamnatin da za ta iya yin aiki da ita, wato karo na farko tun daga lokacin da aka kifar da gwamnatin Mohammad Said Bare kimanin shekaru 22 da suka gabata kenan.

Talla

A wata sanarwa da ya fitar, Asusun na IMF ya bayyana cewa daga yanzu zai soma bai wa sabuwar gwamnatin kasar shawarwari kan yadda ake fasalta tattalin arziki, kuma wannan ne zai share fage wa kasar domin soma samun tallafi daga wasu kasashe da kuma kungiyoyi na duniya.
Rahotanni sun yi nuni da cewa a cikin makon gobe ne kasashen duniya da kuma wasu cibiyoyin kudade na kasa da kasa za su gudanar da taro a birnin Washington na domin duba yadda za a taimakawa kasar ta Somaliya.
To sai dai kamar yadda sanarwar ta Asusun IMF ta ci gaba da cewa, a halin yanzu ba zai iya bai wa Somaliya bashi ba sai bayan ta biya wani tsohon bashin da ke kanta na akalla Dala milyan 352. Tuni dai kasar Amurka ta bayyana aniyarta ta yin aiki da Bankin Duniya da kuma Asusun na IMF domin taimakawa sabuwar gwamnatin da aka kafa a Somaliya

Daga cikin kasashen da suka bayyana aniyarsu ta taimakawa Somaliya sun hada da Amurka, Birtaniya, da kuma kasashen da ke amfani da takardar kudi ta Euro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI