Najeriya

Magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa sun yi rikici a Minna da ke Najeriya.

'Yan wasar Najeriya na murnar cin kofin nahiyar Afirka
'Yan wasar Najeriya na murnar cin kofin nahiyar Afirka Reuters

Wasu matasa da ake kyuatata zaton cewa ‘yan daba ne, sun kai hare hare akan jama a a garin Minna na Jihar Niger a tarayyar Nigeria inda suka jikkata mutane tare da lalata dukiyoyi masu tarin yawa.

Talla

Rahotannin dai sun bayyana rikicin da cewa ya samo asali ne sakamakon gasar kwallon kafa da aka yi tsakanin ‘yan unguwar Limawa da Daji.
To sai dai tuni aka baza jami’an tsaro domin kwantar da hankula sakamakon rikicin da aka yi da makamai dangin adduna da wukake, kamar yadda jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jahar Richar Ogushe ya tabbatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI