Cote d'Ivoire

Ana gudanar da zaben kananan hukumomi a Cote D'Ivoire

magoya bayan wata jam'iyyar siyasa a kasar Cote D'Ivoire
magoya bayan wata jam'iyyar siyasa a kasar Cote D'Ivoire AFP/Issouf SANOGO

A yau lahadi 21 ga watan Afrilu ana gudanar da zaben ‘yan majalisun kananan hukumomi da na manyan yankunan a kasar Cote D’Ivoire.

Talla

Tuni dai magoya bayan jam’iyyar FPI ta tsohon shugaban kasar Laurent Gbgabo sun yi watsi da shiga wannan zabe na yau.

Yakin neman zaben dai ya kawo karshensa a ranar juma’ar da ta gabata, a dan takaitacen yankin neman zabe da ya gudana cikin wani irin yanayi na fargaba.

An dai buda rumfunan zabe ne da misalin karfe 7:30 na safen agogon kasar yayin da ake jiran sakamakon zaben a tsakiyar makon gabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.