Tunisia

Seychelles ta bai wa na hannun damar Ben Ali mafakar siyasa

Shaker El-Mater, na hannun damar tsohon shugaban Tunisia Ben Ali
Shaker El-Mater, na hannun damar tsohon shugaban Tunisia Ben Ali AFP PHOTO/FETHI BELAID

Gwamnatin kasar Tunisia ta bayyana rashin amincewarta dangane da matakin da hukumomin kasar Seychelles suka dauka na bai wa Sakher el-Materi wanda suruki ne ga tsohon shugaban kasar Zeinul-Abidin Ben Ali mafaka siyasar a daidai lokacin da kasarsa ke neman sa domin hukunta shi.

Talla

Shaker El-Metri wanda ke da shekaru 30 a duniya lokacin da aka kori Shugaba Ben Ali daga karagar mulki a shekara ta 2011, tun daga lokacin ne dai ya gudu ya bar kasar sakamakon kiran da al’ummar kasar ke yin a neman a hukunta shi bisa zargin cewa ya yi amfani da karfin ikon surukinsa domin azurta kansa da kuma takurawa jama’a.
Da farko dai wannan dan taliki ya gudu zuwa kasar Fransa ne jim kadan bayan faduwar gwamnatin Ben Ali, kafin daga bisani ya wuce zuwa kasar Qatar. To sai dai duk da cewa gwamnatin Tunisia ta bayar da sammacin kama shi, amma gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ta ci gaba da ba da ba shi damar zama a kasar, yayin da wasu rahotanni ke cewa yana shirin barin kasar zuwa tsibirin Seychelles.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI