Najeriya

Jonathan ya sha alwashin hukunta duk wanda aka samu da laifin kisan Baga

Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan
Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan Reuters/Eduardo Munoz

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya ce ana gudanar da bincike dan gano wadanda suka aikata aika aika a Baga dake Jihar Barno, inda ya sha alwashin cewar duk wanda aka samu da laifi, zai dandani kudar sa. 

Talla

Yayin da yake kaddamar da kwamitin da zai gana da ‘Yan kungiyar Jama’atu Ahlul Sunnah Lida’awati wal Jihad, shugaba Jonathan ya bayayan cewar idan har wani jami’in tsaro ya wuce gona da iri, zai fuskanci fushin hukuma.

“Dole ne a lallubo wadanda suke da hanu a wannan lamari domin su fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.” Inji Jonathan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI